18 Yuli 2020 - 11:31
​China: Amurka Ba Ta Da Hurumin Sake Sabunta Takunkumin Makamai A Kan Iran A MDD

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta bayyana cewa, Amurka tana ta kai gwabro ta kai mari a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, domin ganin an sake sabunta takunkumin hana Iran saye da sayar da makamai.

ABNA24: Kamfanin dillancin labaran Xin Hua ya bayar da rahoton cewa, Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China Hua Chunying ta jaddada cewa, Amurka ba ta da wani hurumi na tilasta kasashe mambobin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, kan su sake sabunta takunkunkumin hana Iran saye da sayar da makamai.

Chunying ta ce; a halin yanzu Amurka ta shagaltu da kokarin ganin ta gamsar da dukkanin mambobin kwamitin tsaro kan su amince da daftarin kudirin da ta gabatar a kan Iran, wanda kuma hakan ya yi hannun riga da kudiri mai lamba 2231.

A cikin kudiri mai lamba 2231 kwamitin tsaron ya amince kan cewa, a ranar 18 ga watan Oktoban 2020, za a dauke dukkanin takunkuman da aka dora ma Iran kan hana ta saye da sayar da makamai, matukar dai tana cikin yarjejeniyar nukiliya, kuma tana yin aiki da yarjejeniyar kamar yadda aka rattaba hannu a kanta.

342/