(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa sudan tana da kashi 3% na wadanda ba musulmi ba na yawan mutanen kasar. Ministan shari’ar kasar ne ya bayyana cewa daga yanzu shan giya a boye ba laifi be ne ga wadanda ba musulmi ba, amma dokar haramta shan giya ta nan daram kan musulman kasar.
Tun shekara 1983 shugaban kasa na lokacin Jaafar Numairi ya kafa dokar hana shan giya, tare da yin bulala ga duk wanda ya sha giya cikinsu.
Nasredeen Abdulbari, ministan shari’ar kasar ne ya bayyana haka a jiya a wata tashar talabijin ta kasar.
Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan dai tana kokarin neman yarda da amincewar kasashen yamma don damar samun tallafin kudaden kyautata tattalin arzkin kasar.
342/