11 Yuli 2020 - 11:20
Jam’iyya Mai Mulki A Ivory Coast Za Ta Matsawa Shugaba Watara Ya Tsayawa Jam’iyyar Takarar Shugaban Kasar

Jam’iyya mai mulki a kasar Ivory Coast tana tunanin matsawa shugaban kasar Alhassan Watara ya tsayawa jam’iyyar takarar shugaban kasa wanda za’a gudanar a karshen wannan shekarar bayan mutuwar magajinsa kuma firai ministan kasar Amadou Gon Coulibaly a ranar laraban da ta gabata.

(ABNA24.com)  Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a cikin watan Marais na wannan shekarar ne shugaban Watara ya bayyana cewa ba zai tsaya takarar shugabancin kasar karo na ukku ba bayan ya share shekaru shekaru 10 yana shugabancin kasar.

Daga bayan jama’iyyarsa ta RHDP ta zabi firai ministan kasar a matsayin wanda zai tsayawa jam’iyyar takarar shugaban kasa a zaben 10 ga watan Octoba na wannan shekarar, sai dai a ranar laraban da ta gabata firai ministan ya mutu yan kwanaki bayan dawowarsa daga kasar faransa inda ya yi jinyar cutar zuciya.

Amma babban sakataren jam’iyyar ta RHDP Adama Bictogo ya fadawa ‘yan jaridu kan cewa suna tunanin tuntubar Shugaba Alhassan Watara don ya sauyan shawararsa ta sauka daga kujrar shugabancin kasar a karshen wannan shekara, tunda kundin tsarin mulkin kasar ta shekara ta 2016 ya ba shi damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar.

342/