9 Yuli 2020 - 12:48
Ivory Coast : Ana Alhinin Rasuwar Fira Minista, Gon Coulibaly

A Ivory Coast, ana ci gaba da alhinin rasuwar fira ministan kasar, Amadou Gon Coulibaly, wanda Allah ya yi wa rasuwa a jiya Laraba, yana mai shakaru 61.

(ABNA24.com)  Tuni shuwagabannin Afrika da dama suka aike da sakon ta’aziyarsu ga shugaban kasar Alhassan Ouatara da kuma al’ummar kasar ta Ivory Coast.

Daga cikinsu akwai Macky Sall, na Senegal, da Rock Roch Christian Kaboré, na Burkina Faso, da Mahammadu Issoufou na Jamhuriyar Nijar, da kuma na kasar Togo Faure Gnassingbé.

Manyan ‘yan adawan kasar ta Ivory Coast da suka hada da Henri Konan Bédié, da Guillaume Soro, da Pascal Affi N’Guessan, duk sun aike da sakon ata’aziya da kuma nuna alhini kan rasuwar mirigayin da suka danganta da babban mai kishin kasa.

Shi dai Fira ministan na Ivory Coast Amadou Gon Coulibaly ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya a wajen taron majalisar ministocin kasar.

Shugaban kasar Alassane Ouattara ya ce ya kadu matuka da rasuwar mutumin da ya bayyana a matsayin kani, kuma da, mai son aiki da kishin kasa.

Kafin rasuwarsa, Mista Coulibaly ne shugaban kasar ya tsayar dan takarar a zaben shugabancin kasar karkashin jam'iyyar RHDP mai mulki a watan Oktoba.

Marigayin, wanda ya shafe shekara uku yana kan kujerar fira minister, ya rasu ne mako guda bayan ya dawo daga kasar Faransa inda ya shafe wata biyu yana jinya sakamakon matsalar ciwon zuciya.

342/