8 Yuli 2020 - 11:20
​MDD: Rasha Da China Sun Yi Fatali Da Wani Daftarin Kudiri Kan Syria

Kasashen Rasha da China sun hau kujerar naki dangane da wani daftarin kuiri da aka kada kuri’a a kansa a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya kan Syria.

(ABNA24.com)  Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a zaman da ya wakana a kwamitin tsaron a jiya, an gabatar da daftarin kudiri kan batun aikewa da taimako zuwa kasar Syria ta hanyar iyakokin Turkiya da Syria, wanda kasashen turai suka amince da shi.

Sai a nasu bangaren kasashen Rasha da China suna ganin zai fi kyau a samar da wasu hanyoyin isar da wannan taimako ta wasu hanyoyin, amma sun amince a bar daya daga cikin hanyoyin da ke kan iyakokin Turkiya da Syria a bude a halin yanzu.

Sai a daya bangaren Rasha ta shirya wani sabon daftrain kudirin wanda za ta mika wa kwamitin tsaron domin yi dubi kafin a kada kuri’a a kansa.

342/