27 Yuni 2020 - 09:08
An Bude Tattaunawa A Tsakanin Iran Da Rasha Dangane Da Kasar Syria Da Kuma Alaka Tsakanin Kasashen Biyu

Jakadan Iran da kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha, sun bude tattaunawa ta hanyar tarho akan kasar Syria da kuma hanyoyin bayar da taimako ga alummar kasar.

(ABNA24.com)  Jakadan Iran da kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha, sun bude tattaunawa ta hanyar tarho akan kasar Syria da kuma hanyoyin bayar da taimako ga alummar kasar.

Tattaunawar bangarorin biyu ta kuma kunshi alaka a tsakanin kasashe biyu da kuma abubuwan da su ke faruwa a cikin yankin gabas ta tsakiya da kuma duniya.

Jakadan na Iran a Rasha Kazem Jalali da kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergei Vershinin sun jaddada muhimmancin warware rikicin kasar Syria sannan kuma da bai wa al’ummar taimakon da suke bukata.

Kasashen Iran, Rasha da kuma Turkiya suna aiki tare domin warware rikicin kasar Syria


/129