(ABNA24.com) Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai ci gaba da shirinsa na janye sojojin kasar 9,500 daga kasar Jamus saboda kin kashewa kungiyar NATO kudade.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa regewar yawan sojojin Amurka karkashin kungiyar tsaro ta NATO a kasar Jamus zai dawo 25,000.
Ba’a sani ba, ko wannan shirin zai tabbata don tuni an ji cewa masu bawa shugaban kasar shawara a cikin jam’iyarsa ta Republican suna sukan matakin da ya dauka. Inda suke ganin yin hakan ya kamar bawa kasar Rasha kyauta.
Kafin haka dai, a shekara ta 2014 kasashen kungiyar tsaro na ta NATO 30, sun amince su kashe kashi 2% na kudaden da suke samu a shekara, a bangaren tsaro, amma da dama basu yi haka ba, daga ciki har da kasar Jamus.
/129
16 Yuni 2020 - 08:33
Lambar labari: 1047197
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai ci gaba da shirinsa na janye sojojin kasar 9,500 daga kasar Jamus saboda kin kashewa kungiyar NATO kudade.