14 Yuni 2020 - 09:46
Hamas Ta Zargi UAE Da Kokarin Samar Da Hulda Da Isra’ila

Hamas Ta Zargi UAE Da Kokarin Samar Da Hulda Da Isra’ila

(ABNA24.com) Kakakin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a kasar Falasdinu da aka mamaye ya soki gwamnatin hadaddiyar daular larabwa kan kokarin da take yi na maida huldar diblomasiyya da Haramtacciyar kasar Isra’ila.

Hazim Kasim kakakin kungiyar ta Hamas ya bayyana haka ne bayan da wata jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto Yusuf Al-Utaiba jakadan kasar Hadaddiyar daular larabawa yana fada a cikin wata makala da ya aikewa jiridar, wacce take cewa “Ko maida hulda ko mamayar yankin yamma da kogin Jordan”.

Kungiyar Hamas ta yi kira ga dukkan kasashen larabawa wadanda suke kokarin kulla huldarjakadanci da HKI da su dakatar da hakan, saboda wannan zai bawa HKI karfin guiwan ci gaba da wulanta falasdinawa da kuma musulmi .


/129