7 Yuni 2020 - 09:24
An Fara Taron Kungiyar Kasashen Masu Arzikin Man Fetur Ta OPEC Karo Na 179

Kungiyar kasashen masu arzikin man fetur OPEC ta fara taronta na 179 a yau Asabar da zimman cimma yarjejeniya ta tsawaita rage yawan man fetur wanda OPEC da OPEC -Plus suke haka na wata mai zuwa.

(ABNA24.com) Kungiyar kasashen masu arzikin man fetur OPEC ta fara taronta na 179 a yau Asabar da zimman cimma yarjejeniya ta tsawaita rage yawan man fetur wanda OPEC da OPEC -Plus suke haka na wata mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayyana cewa a wannan karon saboda cutar Corona ana gudanar da taron ne ta hotunan Badiyo.

Bayan taron na kasashen masu arzikin man fetur ta OPEC dai, ana saran za’a fara taron OPEC -PLUS don tabbatar da bukatar ci gaba da rage yawan man fetur wanda kasashen suke haka da ganga miliyon 9.7 a ko wace rana, saboda kyautata farashin danyen man a kasuwannin duniya.

Ministocin man fetur da kuma na makamashi na kasashen kungiyar OPEC ne suka halattan taron na yau.

Tuni dai, an sami labarin cewa kasashe masu arzikin man fetur wajen kungiyar ta OPEC sun rika sun amince da ci gaba da ragen yawan man da ake haka.


/129