(ABNA24.com) A yau ne zababbun ‘yan majalisar dokokin kasar Iran suka fara gudanar da zamansu na farko a babban ginin majalisar dokokin kasar da ke birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a yayin bude zaman majalisar 11, bayan bude taron da karatun kur’ani da kuma zabar dan majalisa mafi yawan shekaru a matsayin shugaban majalisa na rikon kwarya, an fara ne da karanta sakon jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, wanda shugaban ofishinsa ya karanta.
A cikin sakon nasa, jagoran juyin juya halin ya yi kira ga ‘yan majalisar da su zama masu gaskiya da tsoron Allah a kowane lokaci, sannan su zama masu damuwa da nauyin da hakki na al’umma da yake a kansu, da kuma sauke wannan nauyin ta hanyar aikata abin dace domin amfanin al’umma.
Bayan nan kuma shugaba Rauhani ya gabatar da nasa jawabin, inda a ciki jawabin nasa ya yi ishara da irin muhimmancin da ke tattare da aikin ‘yan majalisar dokoki, tare bayyana cewa aikinsu gishiki ne na dukkanin ayyukan kasa, kamar yadda kuma su ne wakilan al’umma masu wakiltarsu a cikin dukkanin hakkokinsu na kasa.
Wannan dai ita ce majalisa ta 11 tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar Iran.
/129
28 Mayu 2020 - 05:07
Lambar labari: 1040860
A yau ne zababbun ‘yan majalisar dokokin kasar Iran suka fara gudanar da zamansu na farko a babban ginin majalisar dokokin kasar da ke birnin Tehran.