(ABNA24.com) Kwamitin yaki da cin hanci da rashawa da aka kafa a Sudan, domin binciko yadda shugaban kasar ya tafiyar da mulkinsa, ya bayyana cewa kaddarorin dalar Amurka kimanin biliyan hudu ne aka kwace na hambararen shugaban kasar Umar Hassan Al-beshir.
Kwamitin wanda aka kafa a watan Disamban bara, bayan hambarar da shugaban kasar ya ce an kwace kaddarori da kudi na dala biliyan 3,5 zuwa 4 ga Al-bashir da kuma makusantansa.
Kaddarorin sun hada da kudade, gidaje da kuma hanayen jari a wasu kamfanoni, a cewar Salah Manaa, kakakin kwamitin.
Tun dai bayan da ake cafke tsohon shugaban kasar ne yau da wattani 13 ake bibiyar kaddarorin da ya mallaka, sakamakon zarginsa da cin hanci da rashawa.
Kafin hakan dama an gano kimanin dala miliyan 130 boye cikin buhuna a gidansa, baya ga hakan kuma an toshe duk wasu kaddarorin jam’iyyarsa da ‘yan uwa da kuma makusantansa wandanda aka damka wa ma’aikatar kudin kasar.
/129
27 Mayu 2020 - 04:15
Lambar labari: 1040385
Kwamitin yaki da cin hanci da rashawa da aka kafa a Sudan, domin binciko yadda shugaban kasar ya tafiyar da mulkinsa, ya bayyana cewa kaddarorin dalar Amurka kimanin biliyan hudu ne aka kwace na hambararen shugaban kasar Umar Hassan Al-beshir.