(ABNA24.com) A safiyar yau Litinin ce kwamitin yaki da cutar Corona a nan Iran ya amince abude haramin Imam Aliyu bin Musa (a) limami na 8 daga limaman masu tsarki daga iyalan gidan manzon all..(s). Har’ila yau kwamitin ya amince an bude haramin Fatimah Bint Musa (a) da ke birnin Qom a tsakiyar kasar ta Iran.
Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa kwamitin ya rufe wadannan wurare masu tsarki a nan Iran ne, a lokaci guda bayan bullar cutar Corona a kasar watannin kimani biyu da suka gabata. Sannan a halin yanzu za’a ci gaba da budesu ne daga safe zuwa faduwar rana, amma za’a rufesu cikin dare har zuwa wani lokaci.
Banda haka labarin ya kara da cewa za’a bar masu ziyarar wuraren shiga haraman guda biyu ne tare da kula ta sharuddan da kwamitin ya shimfida na kula da matakan kiwon lafiya don hana sake yaduwar cutar a wadannan wurare.
Ya zuwa yanzu dai cutar ta kama mutane kimani dubu 135 a duk fadin kasar , dubu 7 daga cikinsu sun rasa rayukansu, a yayinda dubu 106 kuma suka warke sai kuma sauran wadanda suke jinya ko a asbiti ko kuma a gidajensu.
/129
26 Mayu 2020 - 07:14
Lambar labari: 1040142
A safiyar yau Litinin ce kwamitin yaki da cutar Corona a nan Iran ya amince abude haramin Imam Aliyu bin Musa (a) limami na 8 daga limaman masu tsarki daga iyalan gidan manzon all..(s). Har’ila yau kwamitin ya amince an bude haramin Fatimah Bint Musa (a) da ke birnin Qom a tsakiyar kasar ta Iran.