(ABNA24.com) Jakadan din-din-din na kasar Iran a Majalisar dinkin duniya Majid Takht Ravanchi a lokacin da yake bayani a taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a jiya litinin ya fadi cewa: ya zaman wajibi Amurka da sauran dakarun kasahen wajen da ke kasar siriya su kawo karshen mamayar da suka yi wa kasar Siriya da ya saba ma doka, kuma su dakatar da goyon bayan ’yan ta’adda da sunan yaki da ta’addanci
Har ila yau ya kara da cewa: dole ne kowa ya mutunta iko da yancin siyasa da hadin kan kasar ta siriya, kuma a fili yake cewa Gwamnatin Siriya ba ta amince da zaman dukkan dakarun kasashen wajen da ke kasar ba, don haka dole ne su fice daga kasar.
A gefe guda kuma ya yi watsi da duk wani yunkuri na raba wani bangaren kasar, kana ya yi tir da ci gaba da mamaye Tuddan Golan da Isra’ila ta yi, kuma nuna goyon baya da Amurka ta yi game da ci gaba da mamaye wajen, bashi da tasiri kuma abin kaico ne.
Daga karshe ya jaddada cewa Tuddan Golan mallakin kasar Siriya ne kuma zai ci gaba da zama a matsayin wani bangaren na kasar,
/129
20 Mayu 2020 - 07:34
Lambar labari: 1038614
Jakadan din-din-din na kasar Iran a Majalisar dinkin duniya Majid Takht Ravanchi a lokacin da yake bayani a taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a jiya litinin ya fadi cewa:....