13 Mayu 2020 - 06:20
Iran: An Gudanar Da Jana’izar Sojojin Da Suka Rasa Rayukansu A Lokacin Atisayi

A yau talata ce aka gudanar da jana’izar sojojin ruwan Jumhuriyar musulunci ta Iran su 19, wadanda suka yi shahada a wasan sojojin da aka gudanar a tekun Omman a ranar Lahadin da ta gabata.

(ABNA24.com) A yau talata ce aka gudanar da jana’izar sojojin ruwan Jumhuriyar musulunci ta Iran su 19, wadanda suka yi shahada a wasan sojojin da aka gudanar a tekun Omman a ranar Lahadin da ta gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Iran ta bayyana cewa an gudanar da jana’izar ce a garin Chabahar na bakin ruwan tekun Farisa a yau Talata, tare da halattar manya-manyan jami’an sojoji da kuma gwamnatin kasar.

Banda sojoji 19 da suka yi shahada dai, akwai wasu 15 wadanda suka sami raunuka daban-daban, wadanda kuma suke jinya a asbitocin kasar.

Majiyar sashen yada labarai na rundunar sojojin ruwan ta kasar ta bayyana cewa tuni an kafa kwamiti bincike don gano yadda hatsarin ya auku kafin a san matakan da za’a dauka kan Lamarin.

Sojojin Iran sun saba gudanar da atisanyen soje a mashigar ruwa ta Hurmoz wacce daga nan ne kashi 20% na danyen man fetur da ke shiga kasuwannin duniya ke wucewa don tabbatar da tsaron mashigar.


/129