11 Mayu 2020 - 06:06
CDC : Yawan Masu Cutar Covid-19 A Afrika Ya Kai 60,657

A Afrika, yawan masu kamuwa da cutar Korona, a wannan Lahadi, ya kai dubu 60 da 657 a kasashen 53 na nahiyar.

(ABNA24.com) A Afrika, yawan masu kamuwa da cutar Korona, a wannan Lahadi, ya kai dubu 60 da 657 a kasashen 53 na nahiyar.

Alkalumman wadanda kuma cutar ta kashe ya kai 2,223 a fadin nahiyar, a cewar hukumar hana yaduwar cutuka ta kungiyar tarayya Afrika CDC, ta sanar.

Baya ga hakan a cewar hukumar akwai mutum 20 792 da suka warke daga cutar

Kasashen Afrika ta kudu, da Masar sun ne sahun gaba a yawan masu kamuwa da cutar, sai kuma kasashen Morocco, Aljeriya, Ghana Najeriya, da Kamaru da kma Guinea dake biye masu.

Bayanai sun ce a daidai lokacin da wasu kasashen Afrika suka fara sassauta dokar kulle da matakan yaki da cutar, har yanzu da sauren rina a kaba wajen ganin bayan cutar a yammacin Afrika.

A hanzu haka dai cutar na yaduwa sannu a hankali a yankin sahel, musamman a kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, inda ake ci gaba da samun masu cutar.



/129