(ABNA24.com) Jakadan Iran a Baghada, Iraj Masjedi ne ya bayyana sakon kyakkyawan fata na Iran ga sabon firai ministan Iraki, Mustafa al-Kazemi, wanda majalisar kasar ta amince da shi a jiya Laraba.
Iraj Masjedi ya yi fatan ganin Iraki ta sami ci gaba da daukaka a karkashin sabuwar gwamantin.
A jiya Laraba ne dai majalisar dokokin kasar Iraki ta kada kuri’ar amincewa da al-Kazemi a matsayin sabon firai minista, haka nan ‘yan majalisar ministocinsa 15 da ya gabatar da su.
An sami halartar ‘yan majalisar 233 daga cikin jumillar 329 da ake da su, a yayin kada kuri’ar amincewa da sabuwar gwamnatin
Hudu daga cikin wadanda aka gabatar da sunayensu a matsayin ministoci ba su sami amincewar ‘yan majalisar ta Iraki ba.
/129
9 Mayu 2020 - 06:29
Lambar labari: 1034841
Jakadan Iran a Baghada, Iraj Masjedi ne ya bayyana sakon kyakkyawan fata na Iran ga sabon firai ministan Iraki, Mustafa al-Kazemi, wanda majalisar kasar ta amince da shi a jiya Laraba.