3 Mayu 2020 - 04:59
​Iran Ta Samu Nasarori Masu Yawa A Yakin Da Take YI Da Cutar Corona

Mataimakin ministan kiwon lafiya da makarantun horar da likitoci na kasar Iran ya bayyana cewa kasar Iran wacce take da kashi 1/3 na gadajen asbitoci wadanda suke a Turai da Amurka, amma ta sami nasarori masu yawa a yaki da take yi da cutar Covid 19.

(ABNA24.com) Mataimakin ministan kiwon lafiya da makarantun horar da likitoci na kasar Iran ya bayyana cewa kasar Iran wacce take da kashi 1/3 na gadajen asbitoci wadanda suke a Turai da Amurka, amma ta sami nasarori masu yawa a yaki da take yi da cutar Covid 19.

Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Qasem Jan Babayi yana fadar haka, ya kuma kara da cewa kasar Iran ce ta fara bayyana samuwar cutar Corona a kasarta, bayan bullarta a kasar China.

Sai dai yawan jami’an kiwon lafiya da kuma hadin kan da ta samu daga mutanen kasar sun taimaka a nasarorin da ta samu a wannan yakin.

Dangane da karancin mutuwar tsoffin mutane sanadiyyar cutar a kasar Iran kuma, babayi ya ce, mafi yawan mutanen kasar suna kula da tsoffinsu ne a gidajensu don haka suna samun kula da ta dace daga danginsu, wanda ya kare su daga kamuwa da cutar.

Sabanin kasashen turai da Amurka inda tsoffi ‘yan shekara 70 zuwa sama suna zaune ne a gidajen kula da tsoffi mutane, wanda ya sa suka kamu da cutar ta Corona da sauri, sannan mafi yawansu suka mutu don rashin samun taimako.

A halin yanzu dai kimanin mutane miliyan 3,400,000 suka kamu da cutar Corona a duniya 239,000 suka rasa rayukansu a yayin da fiye da miliyon daya suka warke daga cutar.



/129