21 Afirilu 2020 - 07:40
​Rauhani Da Sarkin Kuwait Sun Tattauna Kan Muhimman Lamurra A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani da sarkin kasar Kuwait Jabir Ahmad Al-Sabah sun gudanar da wata tattaunawa a yau ta wayar tarho kan muhimman lamurra da suka shafi yankin gabas ta tsakiya.

(ABNA24.com)  Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a yayin taattaunawar tasu, shugaba Rauhani da sarkin Kuwait Jabir Ahmad Al-Sabah, sun tattauna kan shirin da Iran ta gabatar na tabbatar da tsaro a mashigar Hormuz a cikin tekun fasha tsakanin kasashen yankin.

Rauhani ya sheda wa sarkin Kuwait cewa, idan kasashen yankin tekun fasha za su hadu, za su iya tabbatar da tsaro a yankin baki daya ba tare da tsoma bakin kasashen ketare ba.

Ya ce bai kamata kasashen yankin gabas ta tsakiya musamman kasashen yanmin tekun fasha su ci gaba da zama a tarwatse ba, musamman a wannan lokaci da ake bukatar aiki na hadin gwiwa donin tunkarar annobar da ke barazana ga dukkanin ‘yan adam.

A nasa bangaren sarkin Kuwait ya yaba da shawarar da shugaba Rauhani ya gabatar, ya kuma jadadda cewa kasarsa tana goyon bayan wannan shawara, domin a hada kai tsakanin kasashen yankin, ta yadda za su iya tunkarar duk wata barazana ta tsaro, da kuma yin aiki tare domin dakile corona.


/129