(ABNA24.com) Ranar Litini, an sayar da ganga daya a kan kasa da Dala uku ($3), har zuwa ($0), a bangaren New York, farashi mafi kankanta a tarihi.
Faduwar farashin ta samo asali ne sakamakon rashin mabukata sakamakon annobar coronavirus.
Wannan na zuwa ne duk da matsayar da kasashen duniya masu arzikin man fetur na (OPEC) suka cimma kwanan baya kan rage man da suke samarwa da kusan ganga miliyan 10 a ko wacce rana, a wani mataki na farfado da darajar man.
A farkon wannan shekara ta 2020 ana sayar da gangar mai a dala 60.
/129
21 Afirilu 2020 - 07:19
Lambar labari: 1028083
Farashin gangar mai ta yi wata irin mummunar faduwa da ba’a taba fuskantar irinta ba tsawon shekaru, inda farshinsa ya fadi warwas a Amurka.