(ABNA24.com) Jaridar Premium Times ta bayar da rahoton cewa, wannan ne karon farko da AfDB zai tanadi wadannan makudan kudade masu yawa domin bayarwa ga wasu kasashe da manyan masana’antun hada-hadar kasuwanci na nahiyar.
AfDB ya ce zai samar da kudaden daga Babban Banki da sauran manyan cibiyoyin hada-hadar kudade, wadanda bankin zai bai wa kudin ruwan da bai kai kashi 1 cikin 100 ba.
Shugaban Bangaren Bada Lamunin Tsarin CIB na Bankin Bunkasa Kasashen Afrika, Tanguy Clagui ne ya yi wannan bayanin.
Coronavirus ta tsaida bunkasar tattalin arzikin duniya, yayin da kashi 80 cikin 100 na hada-hadar masana’antu da kasuwanci a duniya suka tsaya cak.
Wannan tallafi na bankin AfDB ya zo daidai a lokacin da wasu hamsahakan attajirai musamman a Najeriya suka tashi tsaye wajen r bayar da tallafi ga gwamnati domin kokarin dakile Coronavirus.
342