25 Maris 2020 - 06:26
Coronavirus : An Samu Mutuwar Farko A Saudiyya

A Saudiyya, an samu mutuwar farko sakamakon cutar coronavirus, a daidai lokacin da kuma adadin wadanda ke kamuwa ya karu zuwa 767.

(ABNA24.com) A Saudiyya, an samu mutuwar farko sakamakon cutar coronavirus, a daidai lokacin da kuma adadin wadanda ke kamuwa ya karu zuwa 767.

Wanda cutar ta yi ajalin shi a kasar wani dan kasar Afganistan ne dake rayuwa a yammacin birnin Madina, kamar yadda hukumonin kiwan lafiya na kasar suka sanar.

Saudiyya wacce ita ce kasar da ta fi fama da cutar a kasashen yankin golf, ta ayyana dokar hana fitar dare domin dakile yaduwar annobar.

Ko baya ga hakan dama an rufe wuraren sinima da cibiyoyin kasuwanci da wuraren cin abindi, da dakatar da dukkan sauka da tashin jiragen sama da kuma soke aiki Umara wanda a yayinsa milyoyin masu musulmi daga sassa daban daban na duniya ke taruwa.

Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadi game da yadda cutar ke ci gaba da saurin yaduwa a duniya, inda cutar ta yadu zuwa kasashe 189, ta kuma kama mutane sama da 300,000.



/129