(ABNA24.com) Hukumomi a kasar Burkina Faso, sun ayyana zaman makoki na kwanaki biyu bayan wani hari da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 43 a arewacin kasar.
An kai harin na ranar Lahadi ne a kauyen Barga da ke yankin Yatenga a arewacin kasar, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar a jiya Litinin.
Kafin haka dai Shugaban kasar ta Borkina Faso, Roch Marc Christian Kaboré, ya yi tir da harin da ya ce abin takaici ne.
Ba’a dai kai ga tantance ko suwa ne suka kai harin ba, amma gwamnatin kasar ta ce ta aike da jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da tsaro.
/129
10 Maris 2020 - 10:34
Lambar labari: 1016238
Hukumomi a kasar Burkina Faso, sun ayyana zaman makoki na kwanaki biyu bayan wani hari da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 43 a arewacin kasar.