Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : قدس
Lahadi

29 Disamba 2024

14:22:20
1518051

Waiwaye Cikin Irin Ta'addancin Da Isra'ila Ta Yi A Falasɗinu A Shekara 2024

Falasdinu a cikin shekarar 2024 an samu Shahadar 'yan jarida 202 da jikkatar 400....

Kamfanin dillancin labaran Quds ya fitar da kididdiga daban-daban na hare-haren Isra'ila bayan guguwar Al-Aqsa da kuma kididdigar shekarar da ta ke bankwana wato 2024.

A cikin shekara guda da ta gabata ‘yan jarida 202 ne suka yi shahada a Gaza, yayin da dakarun yahudawan sahyuniya suka kame wasu ‘yan jarida 31, kuma a kididdigar karshe tun farkon guguwar Al-Aqsa, ‘yan jarida 202 ne suka yi shahada yayin da wasu 400 suka ji rauni. Har ila yau, ana tsare da ‘yan jarida 41.

'Yan jaridan da ke aiki a Gaza suna ganin cewa, maimakon su zama garkuwa ga rayuwar 'yan jarida, ta hanyar anfani da rigar aikin jarida da tambarin kafafen yada labarai da aka zana a cikinta kayan sun zama alama da ake nufatarsu da kisa don toshe muryar al'ummar Palastinu da sahyoniyawa ke yi.

Carlos Martínez de la Serena, darektan kwamitin kare hakkin 'yan jarida na kasa da kasa, ya ce: 'Yan jarida a Gaza na fuskantar hadari ami tsamari; Abokan aikinsu a Yammacin Kogin Jordan da kuma yankunan da aka mamaye suna fuskantar barazana, hare-hare da kuma tursasawa da ba a taba ganin irinsa ba don hana muhimmin aikin da suke yi na kawo karshen wannan rikici.

Sami Abu Salem; Wani memba na kungiyar 'yan jarida ta Falasdinu ya yi imanin cewa muddin ba'a samar da iyaka ga Isra'ila ba, za su ci gaba da kashe fararen hula da suka hada da 'yan jarida. Wajibi ne kungiyoyin kasa da kasa su yi Allah wadai da ayyukan Isra'ila, in ba haka ba yahudawan sahyoniya za su ci gaba da kai hari kan kafafen yada labarai da karkatar da gaskiya.

A Falasdinu a cikin shekarar da ta ke kokarin shuɗewa; An samu Shahadar dalibai 8,643 tare da Rushe makarantu 40 gaba daya a shekarar 2024 a Gaza

A jajibirin karshen shekara, kamfanin dillancin labaran Quds ya fitar da kididdiga daban-daban na hare-haren bayan guguwar Al-Aqsa da ke cewa: Yakin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ƴan mamaya a Gaza, wanda ya kwashe sama da watanni 15 ana yi, ya sa daliban wannan yanki na fuskantar cikas ga karatu. An ba da rahoton yanayin jin kai a Gaza yana da matukar muhimmanci kuma samun damar ayyukan ilimi ya zama kusan ba zai yiwu ba.

A cikin shekarar 2024 daliban Falasdinawa 8,643 ne suka yi shahada a Gaza, 13,533 kuma suka jikkata, sannan an kama 457. Haka kuma, malamai 534 ne suka yi shahada, sannan malamai 3128 suka jikkata, sannan an kama malamai 87.

A hare-haren bama-bamai da Isra'ila ta kai makarantun Gaza a wannan shekarar makarantu 59 suka lalace sosai, sannan an lalata makarantu 40 gaba daya.

Bisa kididdigar da ma'aikatar ilmi ta Falasdinu ta fitar, tun bayan fara yakin da ake yi da zirin Gaza, dalibai Palasdinawa 12,799 ne suka yi shahada, yayin da dalibai 21,351 suka jikkata sakamakon hare-haren da gwamnatin sahyoniya ta kai.

Tun farkon yakin gwamnatin sahyoniyawan ta yi ruwan bama-bamai a makarantun gwamnati, jami'o'i, da gine-gine na ma'aikatar ilimi a Gaza 484, inda makarantu 351 suka samu barna mai tsanani, sannan makarantu 133 suka lalace gaba daya. Bugu da kari, an lalata makarantu 65 na UNRWA. A Yammacin Kogin Jordan, Isra'ila ta hari tare da lalata makarantu 109 da jami'o'i 7.

Falasdinu a cikin shekarar da ke nufin shuɗewa Isra'ila ta Rushe masallatai 696

 A jajibirin sabuwar shekara, kamfanin dillancin labaran Quds ya fitar da kididdiga daban-daban na ayyukan ta'addanci Isra'ila bayan guguwar Al-Aqsa a cikin shekarar 2024

Ana amfani da masallatai a matsayin alama ta Addini al'ada ga musulmi baya ga ayyukansu na ruhi da kuma kasancewarsu wurin ibadar yau da kullum, kuma babu wani musulmi da bai san masallaci da irin ayyukansa da anfaninsa ba. Girmama wuraren addini ya zama wajibi akan mabiya wannan addini, sannan sauran addinai musamman ma na Ibrahima suna mutunta wuraren ibadar juna, kuma a ko da yaushe ana ganin wuraren addini wuri ne mai aminci a yayin rikici da yake-yake.

A cikin yaƙe-yaƙe da faruwar bala'o'i, masallatai suna aiki a matsayin wurin ibada, mafaka ga 'yan gudun hijira, kuma a wasu al'ummomi, kamar al'ummar Falasdinu, abin da ake kira meta-identity.

A cikin shekarar da take kokarin shuɗewa gwamnatin sahyoniyawan ta lalata kashi 80% na wuraren ibada na Gaza ta hanyar rusa masallatai 696 gaba daya, kuma an kiyasta wannan adadin barnar da ta kai dala miliyan 300.

Tun bayan fara aikin guguwar Al-Aqsa, Isra'ila ta lalata masallatai 821 gaba daya, sannan ta lalata wasu masallatai 157. Har ila yau, gwamnatin Sahayoniya ta lalata majami'u 3 gaba daya.

Har ila yau, a cikin shekarar dai ta 2024 ma'aikata 250 na wuraren ibada a Gaza ne suka yi shahada, kana an kame fiye da mutane 20 kuma suna cikin gidajen yari na gwamnatin sahyoniyawan...