Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

22 Oktoba 2024

19:42:11
1497257

Shedu Na Tabbatar Da Cewa Saudiyya Na Fitar Da Man Fetur A Asirce Zuwa Ga Isra’ila

Kasashen Jamhuriyar Azarbaijan, Kazakhstan, Gabon sun ba da tallafin man fetur mafi girma ga sahyoniyawan a tsawon lokacin yakin.

Jaridar Oil Change International ta rubuta a cikin wani rahoto cewa daga farkon Oktoba 2023 zuwa Yuli 2024, An tabbaatr da jigilar kashi biyu na man fetur wanda yayi daidai da kashi 3% na jimillar man da aka shigar da shi ga Isra’ila ana aika su zuwa wannan gwamnati da ba a san asalinsa ba, daya daga cikin wanda ake loda shi a Masar da dayan kashin da ake ganin mai yiwuwa daga kasar Saudiyya ne.

Wannan rahoto ya tabbatar da cewa duk da hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan sahyoniya ke ci gaba da kaiwa Gaza da kuma hukuncin da kotun duniya ta yanke dangane da kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa, kasashen Jamhuriyar Azarbaijan, Kazakhstan, Gabon sun ba da tallafin man fetur mafi girma ga sahyoniyawan a tsawon lokacin yakin.