Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: cibiyar
yada labaran Hizbullah ta kasar Lebanon ta watsa bidiyon jawabin kwamandan
shahidan Fa’ad Shukri a taron mayakan Hizbullah.
A cikin gungun mayakan Hizbullah ya ce: Ba za mu taba barin makamanmu ba, addu'a ce da rokon Allah Madaukakin Sarki da ya tabbatar da mu, ya kare mu, ya kula da mu, ya kuma shirya mu mu zama sojojinsa. Alkur'ani shine tsayayyen tafarkinmu. Ku wanzu acikin Ganuwoyinku, ku zauna cikin rigarku ta (yaki), Ku bar makamanku su kasance a hannunku, kuma bari taken ku ya tabbatau.
Fu’ad Shukri ya kara da cewa: Masallatan mu su ne katangayenmu Imam Khumaini (RA) ya jaddada yana mai cewa masallaci shi ganuwa ne. Don haka idan kuna son nasara a fagen fama; Ku tsaya a kan wannan hanya, kada ku bar masallatai.
