Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

21 Faburairu 2024

11:20:50
1439396

Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Taron Walimar Dawowar Jagora Allamah Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) A Abuja Najeriya

Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Taron Walimar Dawowar Jagora Allamah Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Wanda Ke Gudana Yanzu Haka A Filin Wasa Na Ƙasa Wato National Stadium Dake Birnin Tarayya Abuja Najeriya

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Wannan taron yana ci gaba da gudana yanzu haka a Babban filin wasa na ƙasa dake Abuja ya cika harda batsewa da fuskokin dinbi. Al'umma tare da Fuskokin wasu daga cikin wakilan ƴan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a yayin da suka iso muhallin taron.

Wakilan sun haɗa da Shaikh Ahmad Yashi, Bauchi, Shaikh Abdulhameed Bello, Zariya, Shaikh Abbare, Gombe, Farfesa Abdullahi Ɗanladi, Zariya, Shaikh Yakubu Yahaya, Katsina, Shaikh Abusumayya, Abuja, Shaikh Sani, Zuru, Shaikh Adamu Tsoho, Jos da dai sauransu.

A Ɓangaren Ƴan uwa mata a wajen walimar murnar dawowar jagora (H) shima wanda ke gudana yanzu haka a filin wasa na ƙasa wato National Stadium dake birnin Tarayya Abuja ya cika makil.