Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

1 Oktoba 2023

16:32:53
1397116

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Bait (AS) Ta Duniya Ya Halarci Ofishin Jakadanci Iran A Kenya

Har ila yau Babban Shugaban na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) yayin da ya kai ziyara ofishin jakadwncin Iran da ke Nairobi ya jaddada wajabcin kara habaka mu'amalar kimiyya da al'adu tsakanin Iran da Kenya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Ayatullah Reza Ramezani a tafiyar kasar Kenya ya samu tarbar Dr. Ja'afar Barmaky jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a birnin Nairobi tare da wasu gungu na masu kula da al'adu da addini na wannan kasa.

Har ila yau Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya jaddada wajabcin kara mu'amalar kimiyya da al'adu tsakanin Iran da Kenya a yayin halartarsa ofishin jakadancin Iran da ke Nairobi.

Dangane da karatun wasu matasa 'yan kasar Kenya da suke yi a jami'ar Jamia Al-Mustafa da ke birnin Qom, Dakta Barmaki ya ce: ita ma Jami'ar Ahlul-Baiti za ta iya ba wa daliban Afirka kaso mai tsoka tare da yin amfani da damar da ake da su a Kenya don gabatar da kansu.

Ya kamata a lura da cewa Ayatullah Ramezani a ci gaba da shirye-shiryensa a ziyarar da ya kai kasar Kenya, baya ga ganawa da masana al'adu da addini, ya ziyarci wasu cibiyoyin addini na kasar, inda ya halarci taron mai taken "Musulmi Matasa: Imani, Kimiyya, Fasaha da makomar Afirka".