Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

30 Satumba 2023

06:17:17
1396738

Raisi: 'Yan ta'adda Ta Hanyar Aukar Da Ayyukansu Na Matsorata A Pakistan, Suna Son Yada Rarrabuwar Kawuna Ne Kawai A Tsakanin Musulmi

Hakan ya zo ne a cikin wata wasika da Mista Raisi ya aike wa takwaransa na Pakistan, Arif Alawi, inda ya nuna juyayinsa ga gwamnati da al'ummar Pakistan na wadanda wannan harin ta'addanci ya rutsa da su.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya tabbatar da cewa, ‘yan ta’addan bisa jahilcinsu da nesantar koyarwar musulunci mai Koyar da hakuri da juriya suna son yada rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi... dangane da hare-haren ta'addanci guda biyu da aka kai a yankunan Pakistan a jiya Juma'a.


Hakan ya zo ne a cikin wata wasika da Mista Raisi ya aike wa takwaransa na Pakistan, Arif Alwi,ainda inda ya nuna juyayinsa ga gwamnati da al'ummar Pakistan ga wadanda wannan harin ta'addanci ya rutsa da su.


Ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana tabbatar da a shirye take ta tinkari dukkanin nau'ikan ta'addanci da masu tsaurin ra'ayi, tare da yin kira ga al'ummomin duniya musamman ma kasashen musulmi da su tashi tsaye wajen yaki da wadannan munanan ayyuka da kuma kawo karshen ci gaba da faruwar abubuwa masu daci irin hakan"


Idan dai ba a manta ba a jiyan mutane da dama ne suka mutu tare da jikkata wasu da dama a wasu hare-haren ta’addanci biyu da suka kai kan wani jerin gwano na addini da kuma wani masallaci a lardunan Balochistan da Khyber Pakhtunkhwa na kasar Pakistan.


Harin na farko dai ya shafi bikin maulidin manzon Allah ne a kusa da wani masallaci a garin Mastung na lardin Balochistan (kudu maso yammacin Pakistan), inda ya kashe mutane 52 ciki har da wani babban jami'in 'yan sandan Pakistan.