Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

30 Satumba 2023

05:31:18
1396730

Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Da Aka Kai A Yankin Balochistan Na Pakistan

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai a lardin Baluchistan na kasar Pakistan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A ranar Juma'a 29 ga watan Sept, Nasser Kanani, bayan harin bam da aka kai kan tawagar masu taron Maulidin-Nabi (AS) a daya daga cikin garuruwan lardin Baluchistan na kasar Pakistan, yayin da yake yin Allah wadai da wannan ta'addanci, ya mika ta'aziyya ga gwamnati da jama'ar Pakistan, musamman wadanda suka tsira da ransu, kuma ya yi addu'ar samun lafiya da samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.