Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

26 Satumba 2023

20:42:12
1396064

Ranar Goma Ga Watan Rabi’ul Awwal Ita Ce Ranar Da Aka Daura Auren Manzon Allah (SAWA) Da Sayyidah Khadija As.

Ranar Goma Ga Watan Rabi’ul Awwal Ita Ce Ranar Da Aka Daura Auren Manzon Allah (SAWA) Da Sayyidah Khadija As.

               Wanda ya dace ace mafi daukakar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da macen da ta dace da girman mutuntakarsa wacce ta amsa manufofinsa madaukaka, wanda kuma babu wata mace a duniyar talikai da cika hakan sai Sayyidah Khadija As. Saboda abunda ke jiranta na qoqari da himma da haquri.

                Sai Hikimar Allah madaukakin sarki ta so cewa zuciyar Sayyidah Khadija ta karkata zuwa ga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa), kuma ta yi shakuwa da dabi'unsa, har ta nemi aurensa da ita (SAWA)haka ya faru,har ta kai aka daura aurensa da ita a ranar goma ga watan Rabi’ul Awwal kafin aiko shi (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da shekaru goma sha biyar.

Yanayi Da Halayen Ma'auratan

                Sayyidah Khadijah (Allah Ya yarda da ita) ta kasance daga cikin mafifitan matan Kuraishawa, mafi arziqi daga cikin matansu, kuma mafi kyawun su, wanda ko a zamanin jahiliyya ana kiranta da (Dahira) da (Shugabar matayen Kuraishawa).

                Shugabannin Kuraishawa sun nemi aurenta, kuma sun kasha kudi sosai akan neman Aurenta, daga cikinsu akwai: Uqba bn Abi Mu'ait, Al-Salt bn Abi Yahab, Abu Jahal, da Abu Sufyan, amma ta ki su gaba daya, sannan ta nuna sha'awarta ta auren Manzon Allah (saww). Saboda girmansa, da tsatsonsa, da darajarsa, da tsafta, da dabi'un da ba za su misaltu ba, da kyawawan halayensa masu daraja.

Farkon Alakarsu

                Ita ta kasance (Allah Ya yarda da ita) ma’aboiyar kasuwanci da dukiya, sai ta ji labarin halaye da darajojin Manzon Allah (SAWA) da amincinsa da girman darajarsa, kamar yadda ake kiransa da {Assadikul Amiin} a zamanin jahiliyya wato mai “Mai gaskiya da rikon amana” don haka ta yi fatan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance daga cikin wadanda yake yi mata cinikin makudan dukiyarta Domin shedar daya ake masa na gaskiyarsa da kyawawan halaye.

                Don haka sai ta dauki matakin tura wani wanda zai kwadaitar da shi wajen kasuwanci tare da ita da kuma neman ya zo yayi aiki tare da ita cikin kasuwancinta, amma Manzon Allah (SAWA) ya ki amincewa da bukatarta, sai ta aika masa da bukatarta kaitsayen na bukatarta na ​​ya yi aiki tare da ita a cikin harkokinta, kuma shi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yarda.

                Tun daganan sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya kasance mai kulawa da dukiyar da yin kasuwanci da su, yan mai tarayyar aiki da ita domin Manzon Allah SAWA bai taba zama ma’aikacin wani ba ko dan aikin wani ba.

Fara Tunanin Yin Aure

                A lokacin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya dawo daga Sham a kasuwancinsa na farko ga Sayyidah Khadija, kuma tare da shi akwai Maisarah - bawanta- inda suka sami ribar da ta ninninka sama da wacce suka samu a baya, sai Sayyidah Khadiha tayi murna Sosai taji dadi, kuma ta kara tausayawa a cikin lamarinsa cikin shauki sosai na daga abun da taji daga bawanta Maisara game da dabi'unsa, halayensa, jarumtakarsa da juriyarsa da girman darajarsa, don haka darajar Annabi da sonsa ya karu a cikin ranta, ta fara yi wa kanta magana kan aurensa kafin a aiko shi.

Neman Aurenta (AS)

                Imam Jaafar Sadik (a.s) ya ce: “Lokacin da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya so ya auri Sayyidah Khadija bint Khuweylid, sai Abu Talib ya je da iyalansa a tare da shi akwai wata tawagar Kuraishawa har yaa shiga wajen Waraqata bin Nawfal baffan Khadija, sai Abu Talib ya fara magana, ya ce: “Godiya ta tabbata ga Ubangijin wannan gida, wanda ya sanya mu cikin zuriyar Ibrahim da zuriyar Isma’il, kuma ya sanya mu cikin amintaccen wuri, kuma ya sanya mu masu mulki bisa jama'a, kuma ya albarkace mu a kasar da muke cikinta.

                Sannan ya ce lalle wannan dan dan  uwan nawa - ma'ana Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) - yana daga cikin wadanda ba za a iya kwatanta shi da wani mutum daga cikin Kuraishawa ba face ya fi shi girma, kuma bay a da tsara a cikin halittu, duk da cewa ya kasance mai karancin dukiya, to amma dukiyar kayna aro ce. Kuma inuwa ce mai gushewa. Yana bukatar auren Khadija kuma itama tana bukatarsa, hakika mun zo maka muna masu nema masa aurenta da yardarta da umurninta, kuma sadakin yan kaina iyaka yadda ku ka bukata a yanzu ko nan gaba, kuma yana gareshi – Na rantse da Ubangijin wannan gidan - yana da babban arziki, da addinin gaskiya da cikakken ra'ayi.

                Sai Abu Talib ya yi shiru, sai baffanta ya yi magana yami kai koma sai ya kasa ba da amsa ga Abu Talib, sai ya kasance cikin rudanin yadda zai ce, kuma shi mutum ne daga cikin malamai, sai Khadija ta ce: Ya baffa, duk da cewa kai kaine mafi cancanta da rayuwata fiye da ni wajen shaida, ba ka fi ni cancanta da kai ba, na aurar da kaina wa Muhammad, kuma sadaki yana kaina, don haka ka umurci kawunka ya yanka rakumi ya ciyar da ita.

                Abu Talib ya ce: Ku shaida akanta na amintar da tai yarda da Muhammadu da lamunin sadakinta a cikin kudinta.

                Wasu daga cikin Quraishawa sai suka ce: Kai! Mata ne zasu bada sadaki ga maza? Abu Talib ya fusata sosai, ya tashi tsaye, yana daga cikin wanda mazaje suke ganin kwarjininsa, kuma suna masu qin ganin fushinsa, sai ya ce: “hakanzai faru idan mazajen sun kasance misalign irin dan dan uwan nan nawa, ta nemi mazaje masu tsada da mafi girman sadaki. Kuma dã sun kasance kamar ku, bã zã aura musu fãce da mafi girman sadaki. Sai Abu Talib ya yanka rakumi, sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya tare da iyalansa.