Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

24 Satumba 2023

08:19:06
1395460

Shin Mu 'Yan Shi'a Ne Ko Masoya Ahlul Baiti?/ Amsar Daga Imam Hasan Askari As

A cikin wani dare muna cikin hidimar Imam Askari (a.s) - a lokacin ne mai mulkin wannan zamanin ya girmawa da rusunawa ga Imam (a.s.) kuma mutanen da ke tare da shi su ma suna girmama shi - kwatsam sai ga gwamnan garin ya zo wucewa, sai ga shi a tare da shi akwai wani mutum daure da hannayensa, shi ne sai yaga Imam (a.s.) a tsaye a saman gidansa (gidan bene ne) ana iya ganinsa daga waje, idanunsa suka kai gare shi, sai ya sauka daga abu hawansa saboda girmamawa ga Imam As.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - A yayin tunawa da shahadar Imam Hasanul Askary As ya Kawo maku wata ruwaya da aka ruwaito dangane Da Hakikanin Kasancewar mutum Dan Shiga ne ko masoyi Ga Ahlul Baity As cewa, A cikin tafsirin Imam Hasan Askari, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, akwai wani hadisi da Abu Yaqub Yusuf bin Ziyad da Ali binu Sayyar suka ruwaito, wadannan ma’abota daraja guda biyu suna cewa:

A cikin wani dare muna cikin hidimar Imam Askari (a.s) - a lokacin ne mai mulkin wannan zamanin ya girmawa da rusunawa ga Imam (a.s.) kuma mutanen da ke tare da shi su ma suna girmama shi - kwatsam sai ga gwamnan garin ya zo wucewa, sai ga shi a tare da shi akwai wani mutum daure da hannayensa, shi ne sai yaga Imam (a.s.) a tsaye a saman gidansa (gidan bene ne) ana iya ganinsa daga waje, idanunsa suka kai gare shi, sai ya sauka daga abu hawansa saboda girmamawa ga Imam As.

Sai Imam Askari (a.s) ya ce masa: “Ka koma kan abun hawanka sai ya koma alhali yana mai risniwa ta bangirm ga Imam As, sai ya koma wurinsa, watau a kan abun hawansa, sai ya ce: “Ya kai dan Manzon Allah, na kama wannan mutumin a daren yau a kusa da wani shagon canjin kudi ina tunanin yana kokarin son bude wani shago hanya ya yi sata. Ni kuma kawai saboda haka na so na yi masa bulala - kuma wannan shine aal’ada ga duk wanda na kama yana sata, sai na yi masa bulala hamsin ga wanda ake tuhuma da na kama don a hukunta shi don kada ya aikata wani babban laifi bayan haka - sai ya ce da ni: Ka ji tsoron Allah, kar ka aikata abin da zai haifar da fushin Allah, hakika ni ina daga cikin ‘yan Shi’ar Ali binu Abi Talib kuma ‘yan Shi’ar wannan Imam mai girma, mahaifi ga wanda ya zai bayyana ya tsayar da adalci da umurnin Allah.

Sai na kyale shi na ce: Zan kai ka wurin Imam (a.s) idan ya tabbatar da maganarka cewa kana cikin ‘yan Shi’arsa, zan sake ka, idan kuma ka yi karya, zan yi maka bulala dubu Zan datse hannuwanku da kafafunku, to yanzu na kawo shi gabanku, shin yana cikin ‘yan Shi’ar ku kamar yadda ya yi da’awa?

Imam Hasanul Askari (a.s) ya ce:

Ina neman tsarin Allah, ta ina wannan ya zamo daya daga ‘yan Shi’ar Ali binu Abi Talib? Allah ya damkashi shi a hannunka domin yana riyawa a tunaninsa na cewa yana cikin ‘yan Shi’ar Sayyidina Ali (AS).

Gwamnan ya ce: Ka hutashsheni, yanzu zan masa bulala dari biyar, kuma babu abin da zai hana ni. To bayan ya tafi da shi cen nesa, ya umurce ma’aikatansa da su kwantar da shi a ƙasa su bulaleshi.

Wadannan mutane biyu sun sauke bulalarsu akan shi da nufin dukansa, amma ba ta same shi ba, duk inda su kai don su same shi amma sai su sami kasa. Hakim sai yaji haushi ya ce da su: tir da ku kuna dukan kasa ne mamadin ku da ke shi? Ku zane wannan mutum ta bayansa da kugunsa, suka sake yunkirin dukansa a bayansa da kugunsa, amma a wannan karon ma sai suka ga hannayensu sun kuskure suna bugar juna suka yi ta ihu da kururuwa.

Sai gwamnan ya ce musu: Kaicon ku, kuna hauka ne? Me yasa kuke dukan kanku? Suka ce: ku daki wannan mutumin da ke kwanc a kasa, kuma ba za a kasa na ce. Sai su kace ai shi muke kokarin yi bama nufar komai sai shi, muna bugawa amma sai hannayenmu su karkace ba tare da ikonmu ba, har bugun ya same mu.

Gwamnan ya kira wasu jami’ansa hudu ya kara da wadannan guda biyu ya ce: Ku kewaye shi ku yi masa duka gwargwadon iyawar ku, sai mutanen shidan suka kewaye shi suka ta daga bulala su yi masa duka, amma a wannan karon sai bulala ta juye sami mai mulkin. Ya sauko daga kan abin hawansa yana yin ihu da kururuwa: Kun kashe ni, Allah ya kashe ku kuma, me kuke yi hakane!? Sai suka ce: mu fa ba ma bugun kowa sai wannan mutumin amma ba mu san dalilin da ya sa hakan ya faru ba?

Sai gwamnan ya ce a ransa: Watakila mutanen nan sun hada baki, sai ya sanya wasu mutane su yi wa wannan mutum duka, amma Suma suka bugi mai mulkin, ya sake cewa: kaitonka, me yasa kuke min duka? Suka ce: mun rantse da Allah, ba mu daki kowa ba ban da wannan mutumin.

Sai gwamnan ya ce: Kun ji min rauni a kaina da fuskata, idan ba ku buge ni ba, daga ina ne wadannan raunukan suka fito? Suka ce: "Ka karye hannayenmu idan mun nufe ka da hakan." Mutumin da aka kama ya ce wa mai mulki: Ya kai bawan Allah, ba ka da kula da lura ka dauki darasi daga wannan ni'imar da aka yi mini na tunkude min dukan bulalar? Kaitonka, ku mai da ni wurin Imam (a.s) ka aikata duk abin da ya umarceka akaina.

Sai gwamnan ya dawo da shi wurin Imam (a.s) ya ce: Ya dan Manzon Allah, lamarin wannan mutumin yana da ban mamaki, a daya bangaren kuma kun musanta cewa shi dan Shi'ar ku ne - kuma duk wanda ba dan Shi'ar ku ba ne babu makawa dan shi'ar Iblis ne kuma makomarsa tana cikin wuta, a daya bangaren kuma na lura tare da ganin mu'ujizozi daga wajensa wadanda suka kebanta da annabawa.

Sai Imam (a.s) ya ce:

Ka ce: Ko kuma magadan annabawa (wato bayyana mu'ujizozi bai kebanta ga annabawa ba, a'a magadansu na hakika suna iya kawo mu'ujiza). gwamnan sai ya gyara maganarsa tare da kara jumlar da Imam (a.s.) ya fada.

Sai Imam Askari (a.s.) ya ce wa gwamna: Ya bawan Allah, wannan mutumin ya yi karya da cewa shi yana daga cikin ‘yan Shi’armu, karyar da in ya fahimce ta kuma ya fade ta da gangan to da ya sha dukan ukubarka, kuma da ya kasance a gidan yarin karkashin kasa tsawon shekara talatin, amma Allah ya ji tausayinsa domin ya yi amfani da kalmar a kan abin da ya yi niyya, kuma bai yi karya da gangan ba, kai kuma bawan Allah, ka sani Allah ne ya cece shi daga hannunka, ku bar shi ya tafi, domin yana daga cikin masoyanmu da masu girmamamu, duk da cewa ba ya cikin 'yan Shi'armu.

gwamnan ya ce: a gare mu wadannan kalmomin duk daya suke, to menene bambancinsu? Imam (a.s) ya ce masa:

الفرق أن شیعتنا هم الذین یتبعون آثارنا، و یطیعونا فی جمیع أوامرانا و نواهینا، فأولئک من شیعتنا. فأما من خالفنا فی کثیر مما فرضه الله علیه فلیسوا من شیعتنا.

banbancin anan shine su ‘Yan Shi’armu su ne masu bin ayyukanmu, suke yin aiki da umurninmu, suke nisantar abin da muka haramta, amma wadanda suka saba mana a da yawa daga cikin abubuwan da Allah Ya wajabta musu, to su ba Shi’armu ba ne.

Sai Imam (a.s.) ya ce wa gwamna: kai ma Kuma ka yi karya da idan da gangan ka aikata Allah zai azabtar da kai da bulala dubu da shekaru talatin a gidan yarin karkashin kasa.

Sai sarki ya ce: mene ne wannan karyar da nayi ya dan Manzon Allah?

Imam (a.s) ya ce: Kun dangana mu'ujizar da kuka gani ga wannan mutum, alhali kuwa mu'ujizar ba daga gareshi ba ne, sai ita aikinmu ce daga garemu ta ke wacce Allah ya saukar da ita game da shi domin ya bayyanar da ikonmu da hujjarmu kuma ya bayyana girmanmu da darajarmu, idan kuwa har ka ce kaga mu'ujizai game da shi - kuma da ba ka danganta aikin da shi ba - da ban yi musun hakan ba. Shin Annabi Isa As da ya raya wani mutum shi ba Mu'ujiza ba ce yin hakan? Shin wannan mu’ujizar aikin wannan mataccen ne ko na Isa? Shin tabon da yayi sifar tsuntsu da shi ya koma Tsuntsu da izinin Allah shin wannan mu'ujizar aikin tsuntsun ne ko Isa? Ashe ba mu’ujiza ba ce ba abunda ya faru wadanda aka shafe su ak mayar da su Birrai? Shin wannan mu'ujiza aikin Birai ne ko kuwa annabin wancan lokacin?

Hakim ya ce: “Astagfirullah Rabbi wa Atubu Ilaihi” “Ina neman gafarar Allah da komawa gare shi”.

Sai Imam Askari (a.s.) ya ce wa wancan da ya yi da’awar shi’ar Ali binu Abi Talib (a.s) ne:

Ya Abdullahi kai ba dan Shi'ar Ali (AS) ba ne, amma kai kan daga masoyansa ne.

Ya kai bawan Allah, kai ba dan Shi'ar Ali binu Abi Talib (AS) ba ne, amma kana cikin abokansa.

Lallai ‘yan Shi’ar wancan Imam su ne wadanda Allah Ta’ala Ya ce:

" والذین آمنوا و عملوا الصالحات اولئک أصحاب الجنة هم فیها خالدون." ( بقره/82)

"kuma Wadanda suka yi imani suka aikata ayyukan qwarai su ne 'yan Aljanna suna masu madawwama a cikinta." (Bakara: 82).

هم الذین آمنوا بالله و وصفوه بصفاته، و نزهوه عن خلاف صفاته و صدقوا محمداً (ص) فی أقواله و صوبوه فی کل أفعاله، ورأوا علیاً بعده سیّداً إماماً و قرماً هماماً لا یعدله من اُمّة محمد(ص) أحد، ولا کلهم إذا جمعوا فی کفّه یوزنون بوزنه، بل یرجّح علیهم کما ترجح السماء و الأرض فی الذرّة.

 ‘Yan Shi’a su ne waxanda suka yi imani da Allah, suka siffanta shi da sifofin da shi da kansa ya siffanta kansa, kuma suka tsarkakeshi daga sauran sifofin da suka saba masa da tsarki da kyau, suka kuma yarda da gaskata Muhammadu (SAW) a cikin dukkan fadinsa, kuma kuma sukai koyi da shi a dukkan aikinsa. kuma sukai yi imani da cewa Ali (a.s.) shi ne shugaba kuma limami wanda babu tamkarsa acikin Al’ummar Muhammad Sawa dukkan bayansa, kuma shi mutum ne mai girma wanda babu wani daga cikin al'ummar Muhammad (s.a.w) da ya kai shi, kai ko daa ace za’a gaba dayansu za’a sanya su a tafin ma’auni gudaa a sanya Ali (a.s) a dayen tafin to tafin Ali As zai rinjayi na su yayi masu fifiko a kansu, kai zai masu rinjaye kamar yadda sama ta yiwa kasa fifiko yayin da aka sanya su a ma’auni.

Kuma ‘yan Shi’ar Ali (a.s.) su ne wadanda akan tafrkin Allah ba su da cewa mutuwa za ta zo musu, ko kuma su fada tarkon mutuwa, ‘yan Shi’ar Ali (a.s) su ne wadanda suka fi son dan'uwansu a kan kawunansu ko da sun kasance mabukata Kuma su ne wadanda ba zaka taba ganinsu a wurin da Allah Ya haramta na ba, kuma za ka ga wunin da Allah yayi umarni da shi ba zak samu basa nan wajen ba.

Kuma ‘yan Shi’ar Ali binu Abi Talib (a.s) su ne masu koyi da shugabansu Ali (a.s.) wajen girmama ‘yan’uwansu muminai da girmama su.

Kuma abin da na fada ba maganata ba ce, maganar Manzon Allah (S.A.W) ce, kuma wannan shi ne umurnin Ubangiji da ya ce: “" وعملوا الصالحات"” yana nufin bayan na yi iqirari da tauhidi da imani da Annabci da Imamanci suna cika dukkan ayyuka da wajibai na Ubangiji, kuma a gaba ga wadanna ayyukan akwai ayyuka guda biyu;

Na daya shi ne biyan hakkokin da bukatun ‘yan’uwa na addini, na biyu kiyaye takiyya da rashin bayyanar da imaninsa a gaban makiyan Allah domin kare rayuka da dukiyoyinsa.

Madogara: Tafsirin Imam Askari, juzu'i na 7, shafi na 316/Bihar al-Anwar, juzu'i na 68, shafi na 160/Tafsir Burhan, juzu'i na 4, shafi na 23.