Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

19 Satumba 2023

08:49:05
1394504

Godiya Da Girmamawa Daga Shugaban Majalisar Ahlul Baiti (A.S) Ta Duniya Bisa Ga Karramawar Da Gwamnati Da Al'ummar Iraki Suka Yi Wa Maziyarta Arbaeen.

A cikin wata wasika da ya aike wa firaministan kasar Iraki, Shugaban Majalisar Ahlul Baiti (A.S) Ta Duniya ya yaba da kokarin gwamnati da al'ummar kasar Iraki da kuma masu alfarma na wannan kasa na karbar bakuncin maziyartan Arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Shugaban Majalisar Ahlul Baiti (A.S) Ta Duniya a wata wasika da ya aikewa firaministan kasar Iraki Dr.Mohammad Shi'a Al-Sudani, ya yaba da wannan matakin kokarin gwamnati da al'ummar kasar da kuma wuraren ibada na wannan kasa na yin maraba da maziyartan Arbaeen.


Nassin wasikar Ayatullah Riza Ramezani shine kamar haka;


Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai


Mai Girma Dr. Mohammad Shia Al-Sudani


Mai Girma Firayim Ministan Iraki


Salamun Alaikum


Ina rokon Allah ya baku lafiya da nasara a tafarkin hidimar Musulunci da mazhabar Ahlul Baiti (AS).


Abin farin ciki ne cewa a madadin kaina da kuma na wakilan majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul Baiti (a.s.) da dukkan maziyartan Sayyidina Aba Abdullahil Husain (a.s) na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sauran daukacin mabiya mazhabar Ahlul Baiti (a.s) gare ku da gwamnati na ke mika godiyata da girmamawa ga al'ummar Iraki bisa gagarumin tarba da karimcin ga masoya maziyarta mabiya shugaban Shahidai na karbar bakuncin 'yan'uwansu da 'ya'yan al'ummar kasar Iraki masu daraja su kayi a lokacin Arba'in Husaini.


Har ila yau ina mika godiyata ga mai martaba da dukkanin jami'an gwamnati da hukumomin tsaro masu alaka da su, musamman a lardunan Najaf Ashraf, Karbala da sauran lardunan kudu da kuma Kufa na Atbat da Mawakb Husaini saboda kwazon da suka nuna da kokari a lokacin da Maziyarta suke kasarku mai albarka.


Ina rokon Allah da ya kare kasar ma'asumai (AS) da wurare masu tsarki na Musulunci da kariyarsa, ya kuma kara maku kwarin gwuiwa wajen hidimtawa al'ummar Musulunci da mazhabar Ahlul Baiti (AS).


Tare da dukkan girmamawa


Dan uwanku


Redha Ramezani

Shugaban Majalisar Ahlul Baiti (A.S) Ta Duniya 

.........................