Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

18 Satumba 2023

14:59:24
1394362

Amurka: Fadar White House ta amince da sakin fursunonin Amurkawa tare da sakin kadarorin Iran

Amurka: Fadar White House ta amince da sakin fursunonin Amurkawa tare da sakin kadarorin Iran

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya nakalto maku daga kamafanin yada labaran -IRNA- cewa Fadar White House ta tabbatar da sakin wasu Amurkawa biyar bisa sakin wasu Iraniyawa biyar tare da sakin kadarorin Iran a Koriya ta Kudu.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, shafin yada labarai na yanar gizo na "Hill" ya bayar da rahoton cewa, a ranar Litinin din nan ne aka sako wasu fursunonin Amurkawa 5 da ke Iran a matsayin musayar fursunoni biyar na Iran da kuma dage takunkumin da aka kakaba wa wasu kadarorin Iran din na dala biliyan 6.


Wani babban jami'in fadar White House da bai so a bayyana sunansa ba, ya shaida wa kafar yada labaran Amurka cewa: "A safiyar Litinin din nan wasu fursunoni biyar na Amurka da wasu 'yan uwansu biyu sun tafi Doha ta jirgin saman Qatar domin tafiya Washington daga nan."


Wannan jami'in na Amurka ya sanar da yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin Iran da Amurka a matsayin sakamakon doguwar tattaunawa mai cike da sarkakiya.


A 'yan sa'o'i kadan da suka gabata, kamfanin dillancin labaran reuters, ya nakalto majiyoyi masu cikakken bayani cewa an mika fursunonin na Amurkan zuwa wani jirgin saman Qatar domin su bar Iran.


Tun da farko, kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar kasar Qatar cewa, jirgin kasar Qatar ya shirya kai wasu fursunoni biyar na Amurka da wasu 'yan uwansu biyu zuwa birnin Doha da safiyar yau a kasar Iran.


Ita ma wannan majiya mai tushe ta sanar da mika kadarorin Iran na dala biliyan 6 daga Koriya ta Kudu zuwa asusun banki a Doha.


Game da musayar fursunoni tsakanin Iran da Amurka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kanani ya bayyana a yau cewa: Tsarin aiwatar da yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma kan batutuwan biyu na kawar da takunkumin tattalin arziki da aka yi wa kadarorin kasar Iran A Koriya ta Kudu da musayar fursunoni sun ci gaba mataki-mataki kuma cikin sauri, kuma muna fatan a yau za mu ga tarin kadarorinmu daga Koriya ta Kudu.


Ya kara da cewa: A kan haka ne a wannan rana za a yi musayar fursunoni sannan za a sako fursunonin Iraniyawa 5 daga gidajen yarin Amurka. Duk da cewa 2 daga cikin wadannan mutane ne kawai za su koma Iran, kuma mutum daya zai tafi kasa ta uku ta haihuwarsa domin ya kasance tare da iyalansa, sauran mutane 2 kuma sun nuna sha'awar su ci gaba da zama a Amurka, mamadin hakan kuma za a mika fursunoni 5 zuwa Amurka.