Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

17 Satumba 2023

19:31:37
1394183

Hotuna Da Bidiyon Yadda Sojojin Mamaya Su Ka Kai Hare-Hare Ga 'Yan Jarida Da Falasdinawa A Gabashin Gaza

Daruruwan Falasdinawa ne suka gudanar da zanga-zanga a wannan Lahadin domin yin Allah wadai da matakin wuce gona da iri kan masallacin Al-Aqsa da fursunonin da ke cikin gidajen yari.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA ya habarta cewa, a yammacin yau Lahadi, bayan harin da sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan Falasdinawa a kusa da shingen kan iyaka a gabashin zirin Gaza, an jikkata wasu 'yan kasar Falasdinu da wasu 'yan jarida da dama.


Kafofin yada labaran Falasdinu sun ce sojojin mamaya sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar a gabashin zirin Gaza, inda suka jikkata 'yan jarida uku da wasu 'yan kasar sakamakon wannan harin.


Daruruwan 'yan kasar ne suka gudanar da zanga-zanga a kusa da shingen kan iyaka da ke gabashin birnin Gaza, da garuruwan Rafah da Khan Yunis, da ke kudancin zirin Gaza, da Jabaliya da kuma gabashin sansanin Burj da ke tsakiyar yankin, domin yin Allah wadai da matakin hare-haren wuce gona da iri kan masallacin Al-Aqsa da kuma fursunonin da aka kama masu ake tsare da su.


Anan kasa akwai hotuna da Bidiyon ‘Yan mamaya na yahudawan sahyoniya inda suka auna ‘yan jarida kai tsaye nufin illatasu.