Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

13 Satumba 2023

11:51:31
1393361

Jakadan Saudiyya A Tehran: Dangantaka Saudiyyah Da Iran Za Ta Yi Karfi A Dukkan Fannoni

Dangantakar tsakanin Kasar Iran da Saudiyya za ta kasance mai karfi a dukkanin bangarori da suka hada da kasuwanci, tattalin arziki da zuba jari.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Abdullah bin Saud Al-Anzi, sabon jakadan Saudiyya a kasar Iran ya bayyana jin dadinsa a lokacin da aka fara wani sabon babi na dangantakar kasarsa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya kuma jaddada cewa, dangantakar za ta kasance mai karfi a dukkanin bangarori da suka hada da kasuwanci, tattalin arziki da zuba jari.

Abdullah bin Saud Al-Anzi, wanda ya halarci bikin cika shekaru 74 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Tehran a yammacin jiya, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran: Alhamdulillah dangantakar da ke tsakanin masarautar Saudiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dawo Wadannan alakoki za su kasance masu inganci, masu karfi da tushe bisa maslaha guda, mutunta juna da kyakkyawar makwabtaka. Wadannan alakoki za su yi karfi a dukkan fannonin kasuwanci, tattalin arziki da zuba jari.