Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Ayatullah Jannati yayinda yake jawabi a wajen taron Shugabannin majalisar kwararrun jagoranci ya fuskantar da bayaninsa ga wadanda suka halarci wannan taro na Arbaeen da cewa: Ku dauki kanku a matsayin jakadun Arbaeen kuma ku kula tare da kuma kare ilimi da ruhiyya da aka samu daga wannan taro na addini domin ku zama tushen daukaka matsayin ruhi a cikin al'umma.
Yayi kira da ga masu Fahasa da Yada Labarai inda ya ce : Masu fasahar al'adu da kafofin yada labarai na juyin juya hali su ma su tsara yadda za su tunkari shurun kafafen yada labarai na duniya masu mulki dangane da wannan lamari mai girma da kuma daukarsa a matsayin misali na jihadi.
Shugaban majalisar kwararrun jagoranci yayi tsokaci dangane da ganawar da al'ummar lardin Sistan da Baluchistan da kuma kudancin Khorasan suka yi da Jagoran ya bayyana cewa: A cikin wannan ganawar, Jagora ya gabatar da cikakken bayani dalla-dalla kan tsare-tsaren makiya, wanda ya wajaba masu goyon bayan juyin juya halin Musulunci da su yi taka tsantsan a cikin wannan cikakken bincike, su san kuma me ya hau kansu wanda ya kamata su aikata wajen tunkarar dabarun makiya da tsare-tsarensu don su magance su.