Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

13 Satumba 2023

10:32:19
1393355

Mutane dubu 10 sun bata yayin da mutane dubu 36 suka rasa matsugunansu.

Adadin wadanda suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a Libya ya kai mutane dubu 6

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya ta sanar da cewa, sama da mutane 5,200 ne suka mutu sakamakon anbaliyar ruwa da ta afku a daya daga cikin biranen gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya nakalto maku daga Kamfanin dillancin labaran IRNA ya habarta cewa a ranar Jiya Talata kakakin gwamnatin hadin kan kasar Libiya karkashin jagorancin Fathi Pasagha, ya sanar da cewa, sama da mutane dubu 5 da 200 ne suka rasa rayukansu a birnin Darna, daya daga cikin garuruwan da anbaliyar ta shafa gabashin Libya.

Dangane da haka, manajan yada labarai na kungiyar agaji ta Red Crescent a birnin Tokrah ya shaida wa Al Jazeera cewa: "Halin da ake ciki a birnin Derna yana da cikin hali mai muni kuma babu alamar rayuwa a cikinsa."

Har ila yau, hukumar kwallon kafar Libya ta sanar da cewa anbaliyar ta yi sanadin mutuwar 'yan wasan kasar 4.

Ministan sufurin jiragen sama na kasar Libya kuma mamba a ma'aikatan rikicin kasar Libya ya shaidawa kamfanin dillancin labaran reuters a yau cewa adadin wadanda suka mutu a birnin Darna na da yawa kuma ana ganin gawarwakin ko'ina.

Ya kara da cewa: Ban wuce gona da iri ba idan na ce kashi 25% na birnin Derne ya bace.

A yau, a kididdigar da ya yi na baya-bayan nan, ministan lafiya na kasar Libya ya sanar da mutuwar mutane fiye da 3,000, amma a lokaci guda ya yi hasashen adadinsu zai karu zuwa dubu 10.

A nasu bangaren, kungiyar agaji ta Red Cross ta sanar a yau cewa sama da mutane 10,000 ne suka bace a Libya.

Garuruwan Gabashin kasar Libya sun ga mummunar Anbaliyar "Daniel" a ranar Litinin, kuma saboda girman yankin da hakan ta faru da kuma rashin kayan aiki, hukumomin Libya sun bukaci taimakon kasashen duniya.

Libya na bukatar kungiyoyin bincike da ceto inda kasar Masar ke gina gadar sama don ba da taimako ga Libya kuma Hukumar Lafiya ta Duniya ce Halin da ake ciki a Libya bayan anbaliyar na da matukar hadari. Da yake nuna juyayin Amir Abdullahian ga gwamnati da al'ummar kasar Libya bayan bala'in ambaliyar ruwa.

Ina da sakamakon hakan Hukumar kasar Libya ta ayyana kwanaki uku na zaman makoki

Amma a rahoton baya bayan nan Adadin wadanda suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a Libya ya kai mutane dubu 6/Mutane dubu 10 sun bata yayin da mutane dubu 36 suka rasa matsugunansu.

Mataimakin ministan lafiya na gwamnatin hadin kan kasa ta Libya ya sanar da cewa, adadin mutanen da suka mutu sakamakon guguwar Daniel da ta haddasa ambaliyar da ba a taba ganin irinsa ba a gabashin kasar ta Libiya ya kai 6,000.

Wannan jami'in na Libya ya jaddada cewa har yanzu dubban mutane sun bace.

A halin da ake ciki kuma Hukumar Kula da Hijira da mafaka ta Duniya a Libiya ta sanar a ranar Talata cewa akalla mazauna birnin Darna 30,000 da suka fi fama da barnar guguwar Daniel ta raba da matsugunansu.