Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

11 Satumba 2023

02:35:32
1392771

ISIS Sun Kai Mummunan Hari Kan Wasu Gungun Makiyaya A Gabashin Siriya

Kamfanin dillancin labaran Syria ya bayar da rahoton cewa, wasu mutane dauke da makamai masu alaka da kungiyar takfiriyya ta Daesh sun kai hari a yankin Shula da ke kudancin lardin Deir Ezzor a gabashin kasar Siriya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kasar Syria (SANA) ya bayyana cewa, wasu mutane dauke da makamai masu alaka da kungiyar takfiriyya ta Daesh sun kai hari a yankin Shula da ke kudancin lardin Deir Ezzor a gabashin kasar Siriya.

SANA ta kuma ruwaito cewa, a yayin wannan harin ta'addancin, makiyaya shida ne suka yi shahada tare da jikkata wasu biyu.

Yankin Shula mazaunin mutanen kabilar Albusraya ne; Galibin mazauna yankin na yin kiwon dabbobi a wuraren kiwo na yankin.

A cewar wadannan majiyoyin, 'yan ta'addar ISIS sun daddatsa gawarwakin wadanda aka kashe tare da cinna wa motocinsu wuta, kuma ba su yi wa dabbobin rahama ba.

Yankin hamadar Shula yana kan hanyar Palmyra zuwa Deir Ezzor, kuma kabilar Al-Busraya ba ta taba bawa kungiyar takfiriyya ta ISIS mafaka ba a tsawon shekaru goma da suka wuce.

.........................