Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

10 Satumba 2023

04:31:11
1392523

An Kai Hari Ofishin Jakadancin Iran Da Ke A Birnin Paris

A jiya Asabar 18 ga watan Shahrivar wanda yayi daidai da 09 ga watan Satumba 2023 ne wasu gungun 'yan ta'adda na munafukai suka kai hari da bama-bamai na wuta a kofar ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Paris.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Wanda an kai harin ne yayin da 'yan sandan Faransa ba su dauki wani mataki na tabbatar da tsaron ofishin jakadancin kasar ta Iran ba.

Ofishin jakadancin Iran a birnin Paris yayi bayani dangane da harin da aka kai masu daga bangaren masu adawa da juyin juya halin musulunci.

Bayanin ofishin jakadancin Iran a birnin Paris dangane da harin da aka kai masu wanda masu adawa da juyin juya hali su ka aikata ya zo ne kamar haka yadda Kamfanin dillancin labaran IRNA ya rubuta cewa: Kakakin ofishin jakadancin kasar Iran da ke kasar Faransa ya yi nuni da cewa, halin da ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris na kasar Faransa ke ciki na cikin halin Tsaro sosai, bayan wani mummunan hari da wasu gungun masu adawa da juyin juya hali suka kai musu, inda ya ce babu wani cikas a gudanar da harkokinsa.

Mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin Paris ya sanar da cewa, ana neman wadanda suka kai harin na matsorata da masu adawa da juyin juya hali kan ginin karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris.

A cewar rahoton, a safiyar jiya Asabar wasu mutanen da ba a san ko su waye ba na kungiyoyin masu adawa da juyin juya hali, a wani yunkuri na Matsorata sun kona wasu tayoyi a kofar shiga ofishin karamin ofishin jakadanci na wannan ofishin, tare da haddasa wata ‘yar barna a kofar shiga ofishin jakadancin wannan ginin.


Ya kara da cewa: An kashe gobarar bayan 'yan mintoci kadan tare da halartar jami'an 'yan sanda da na kashe gobara, kuma ana ci gaba da bin hanyar da ta dace tare da ma'aikatar harkokin wajen Faransa da hukumomin 'yan sanda domin bude bincike na shari'a tare da zakulo wadanda suka aikata laifin wannan aika aika.