Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

9 Satumba 2023

10:48:20
1392304

Mutane 632 ne suka mutu yayin da 153 suka jikkata sakamakon girgizar kasar a Marocco

Ma'aikatar cikin gidan kasar Magrib ta sanar a safiyar yau Asabar cewa mutane 296 ne suka mutu yayin da wasu 153 suka jikkata sakamakon girgizar kasar da ta afku a daren Juma'a.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A cewar wannan rahoto, an kuma bayyana cewa gidaje da dama ne suka lalace sakamakon wannan girgizar kasar.

A cewar daya daga cikin mazauna yankunan da girgizar kasar ta shafa, girgizar kasar takai tsawon dakika 20 a karo na biyu bayan girgizar kasar ta farko.

An kuma ji wannan mummunar girgizar kasa a Spain da Portugal.

Ana samun karuwar adadin wadanda suka mutu da jikkata sakamakon girgizar kasar ta Morocco

Adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar Maghrib ya zuwa yanzu ya karu zuwa mutane 632.