Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

9 Satumba 2023

04:52:26
1392239

Shaikh Zakzaky: Gwagwarmayar Imam Husaini (AS) Ita Ce Kadai Hanyar Ceton Bil’adama

Jagoran Harkar Musulunci ta Najeriya ya kuma jajantawa Imamai da Jagoran juyin juya halin Musulunci da al'ummar musulmi bisa sake Zagayowar Arbaeen Husaini (AS).

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayyana muhimmanci da sakon Arba'in Husaini da cewa: Imam Husaini (AS) ya yi sadaukarwa ne don cin nasarar adalci da gaskiya a kan zaluncin duniya tare da tabbatar da cewa Hanyar ceton bil'adama kawai ita ce tsayin daka kan tafarkin Imam Husaini (AS).

Jagoran Harkar Musulunci ta Najeriya ya kuma jajantawa Imamai da Jagoran juyin juya halin Musulunci da al'ummar musulmi bisa sake Zagayowar Arbaeen Husaini (AS).

Sheikh Ibrahim Zakzaky ya jaddada cewa: Mutane a wannan zamani da muke ciki sun fahimci sadaukarwa da tsayin daka da Imam Hussain (AS) ya yi a yunkurin Karbala, inda daga karshe limamin Shi'a na uku ya sadaukar da rayuwarsa kan tafarkin 'yanci.