Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Mahaifi da dansa sun yi shahada sakamakon harbe-harbe da 'yan ta'adda suka yi a yankin Kurangi, yankin da ya fi cinkoson masana'antu a Karachi.
Bayanai na farko sun nuna cewa, 'yan ta'addar takfiriyya sun harbe a wani kantin sayar da litattafai da ke birnin Korangi, wanda a sakamakon haka ne mahaifin da Ɗansa 'yan Shi'a suka yi shahada.
Muhammad Husain da dansa Asad sun yi shahada a wannan harin na matsorata ragage 'yan Ta'adda