Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

6 Satumba 2023

20:24:27
1391745

Juyin Mulki A Kasashen Afirka; Faransa Tana Fuskantar Bijirewa Saboda Nau'in Mulkin Mallakan Da Ta Yi A Baya A Afirka

A cewar jaridar "Washington Post", a yammacin Afirka, 'yan mulkin mallaka na ci gaba da faduwa

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Kimanin wata guda kenan da hambarar da gwamnatin Nijar, lamarin da ya haifar da takun saka tsakanin gwamnatin sojin kasar da kasashen duniya.

Sannan manyan jami'an kasar Gabon sun tsige Ali Bongo, tsohon shugaban kasar, bayan wani zabe mai cike da cece-kuce; Hambarar da shugaban kasar Gabon, wanda a halin yanzu yake tsare a gidan yari, shi ne juyin mulki na bakwai a Afirka cikin shekaru uku, ciki har da juyin mulkin da aka yi a Mali, Burkina Faso da Guinea.

Akwai bambance-bambancen mahalli da dama tsakanin juyin mulki iri-iri a Afirka, amma suna da wata hujja guda daya wacce ba za a iya kaucewa da rufe ido ba akanta: yawaitar kyamar Faransawa da ke kin amincewa da matsayin siyasa a kasashe da dama na yammacin Afirka da kuma a dukkan kasashen nahiyar da suka dandani juyin mulkin daga wqjen Faransa.

Faransa tsohuwar mai mulkin mallaka ce; Hukumomin sojan da suka hambarar da gwamnatocin da suka gabata, sun kara fusata su kan abunda suka gada mai zurfi da sarkakiya na mulkin daular Paris.