Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

4 Satumba 2023

11:25:21
1391056

An Bude Baje Kolin Shahidan Bahrain A Karbala

An bude bikin baje kolin Shahidan Bahrain a Karbala Ma'ali.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Wannan baje kolin ya kunshi hotuna da kwafi na shahidan juyin juya halin Bahrain da kuma ayyukan fasaha masu alaka da su. Sanann an gudanar da wasu shirye-shirye daban-daban a cikin wannan baje kolin.

Ibrahim Al-Aradi, darektan ofishin siyasa na kawancen kasashen Larabawa a ranar 14 ga Fabrairu, ya aike da sakon neman maziyartan Arbaeen na Imamul Husaini da su yi amfani da wannan damar wajen isar da muryar al'ummar Bahrain ta hanyar halartar wannan baje koli.