Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

4 Satumba 2023

11:22:59
1391055

An Rushe Wani Matsugunin 'Yan Ta'adda A Iraki

Dakarun sojin saman Iraki, bayan hare-haren da aka kai a matsugunan 'yan ta'adda, sun kai hari a wani matsuguni a garin Al-Debs na lardin Kirkuk bisa ingantattun bayanan sirri.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A cikin sanarwar da sashen yada labarai na harkokin tsaron kasar Iraki ya fitar, an bayyana cewa, jami'an tsaron kasar na ci gaba da fatattakar 'yan ta'addar da suka aikata muggan laifuka daga kasarsu.

Jami'an tsaron Iraki na ci gaba da bincike tare da kawarwa da bibiyar 'yan ta'addar ISIS a duk fadin kasar domin an tabbatar da sake bullowar kungiyar ISIS da 'yan ta'addar da ke gudun hijira.

Ragowar mayakan ISIS na ci gaba da kai hare-hare a yankunan Baghdad, Salahaddin, Diyala, Kirkuk, Nineveh, Anbar, da dai sauransu.