Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

4 Satumba 2023

08:33:28
1391028

An Kashe 'Yan Ta'addar Al-Shabaab 150 A Somaliya

A wani samame da sojoji suka kai a tsakiyar Somaliya, an kashe 'yan ta'adda 150 na kungiyar al-Shabaab.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Kwanaki biyu da suka gabata, an kashe 'yan ta'adda 20 na wannan kungiya a wani samame ta sama da sojojin Somaliya da kawayenta suka kai ta sama.

Kazalika majiyoyin labarai sun ruwaito a daren ranar Asabar din da ta gabata cewa, an kashe 'yan kungiyar ta'adda ta Al-Shabaab 13 a farmakin da sojojin kasar Somaliyan suka kai a kasar.

Inda aka samu kashe wadannan 'yan ta'adda ne a lokacin farmakin da sojojin Somaliyan suka kai ta sama da ta kasa a lardin "Lower Juba" da ke kudancin kasar.