Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

7 Yuni 2023

11:06:16
1371629

An Kashe Wani Kwamandan ISIS A Peshawar, Pakistan

Majiyoyin labarai sun ba da rahoton mutuwar shugaban kungiyar ta'addanci ta ISIS a birnin Peshawar na kasar Pakistan, a wani samame da jami'an tsaro suka kai.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya nakalto maku cewa, ayyukan hukumar yaki da ta’addanci da ‘yan sanda a yankunan Peshawar, Bajaur da Swat da ke arewa maso yammacin wannan kasa, ya haifar da da mai ido inda ya kai ga mutuwar 'yan ta'adda 5.


Ma'aikatar Yaki da Ta'addanci a Pakistan ta sanar da cewa, an gano tare da kashe wani kwamandan kungiyar ta'addanci ta Da'ish, wanda aka sanya ladan kudi har Rupee miliyan biyu (kimanin dala 6,500) a kansa ga duk wansa ya kawo kansa, a wani samame da jami'an tsaro suka kai masa.


Hukumomin Pakistan a koda yaushe suna musanta wanzuwar kungiyar ISIS a kasarsu, duk kuwa da cewa kungiyar ta'addancin ta dauki alhakin kai munanan hare-hare da tashin bama-bamai a kasar cikin 'yan watannin nan.