Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

7 Yuni 2023

10:58:22
1371626

Bankin Duniya: Talauci Ya Yadu A Afghanistan

Bankin Duniya ya sanar a cikin rahotonsa na shekara cewa: Talauci na tattalin arziki ya yadu a Afghanistan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, babban bankin duniya ya sanar a cikin rahotonsa na shekara-shekara game da yanayin tattalin arzikin kasashen kudancin Asiya: Talauci ya yadu a kasar Afganistan kuma kusan daukacin al'ummar kasar ba su da isasshen abinci saboda rashin isassun kudin shiga.

Rahoton Bankin Duniya ya ce kashi casa'in da biyu cikin dari na mutanen Afghanistan ba su da isasshen abinci da za su ci.

A sa'i daya kuma, bankin duniya ya kara da cewa: hasashen tattalin arziki a kasar Afghanistan ya daidaita tare da dawo da kudaden agaji, kuma ana sa ran karuwar samar da kayayyaki zai yi kyau cikin shekaru biyu masu zuwa.

Kafin haka dai, bankin duniya ya sanar da wasu abubuwa masu kyau game da harkokin tattalin arzikin kasar Afghanistan, da suka hada da kayyade farashin kayan masarufi, kula da darajar kudin kasar, da kara yawan fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, da biyan albashin ma'aikatan cikin lokaci, wannan rahoton ya samu karbuwa daga gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan.

Rahoton da bankin duniya ya fitar kan yawaitar talauci a kasar Afghanistan, ya ce adadin taimakon jin kai da ake ware wa al'ummar kasar a bana ya ragu da kusan kashi 30% daga dala biliyan hudu da miliyan dari shida zuwa dala biliyan uku da miliyan dari biyu.

A cikin rahoton nata na baya-bayan nan, ofishin bayar da agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce adadin mutanen da ke bukatar agaji a bana ya karu da miliyan 500,000 zuwa miliyan 29.

.........................