Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

5 Yuni 2023

03:51:33
1371184

Jerin Taruka Da Ake Cigaba Da Gabatar Dasu Tunawa Da Shekaru 34 Da Wafatin Imam Khumain Qs

Taron jama'a da tattakin da aka yi a wasu garuruwan Iran domin nuna adawa da kamun da aka yi wa Imam Khumaini.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya kawo maku takaitaccen tarihin abunda ya faru a, Zanga-zangar 15 Khurdad da aka yi a Qom, Tehran da ta rikide tayi tsamari inda aka kashe da jikkata wasu da dama.


An kama Imam ne saboda jawabin da ya yi a makarantar Faiziyah akan Muhammad Reza Pahlawi, Shah na Iran a lokacin. A cikin wannan jawabi an kwatanta gwamnatin lokacin da gwamnatin Yazidu. Imam Khumaini saboda wasu gungu na jama'a ya ayyana wannan rana a matsayin makokin jama'a na har abada, don haka ranar 15 Khurdad hutu ce a hukumance a kalandar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.


A safiyar ranar 15 ga watan Khurdad ne aka sanar da al'ummar Qum da wasu garuruwa game da kamun da aka yi wa Imam Khumaini tare da fara zanga-zanga. A Tehran, daliban jami'ar Tehran sun rufe azuzuwa tare da shiga zanga-zangar mutane masu sayar da kayyyaki tare da rakiyar wasu fitattun mutane irin su Tayyib Haj Rezaei da Haj Ismail Rezaei suma sun tashi daga tsakiyar gari suka shiga cikin masu zanga-zangar. Masu zanga-zangar, wadanda adadinsu ke karuwa a lokaci guda, sun so su mamaye muhimman cibiyoyin gwamnati kamar fadar Marble, Sashen Rediyo, Sashen Makamai na Sojoji, da dai sauransu. Hakanan suma kuma ‘yan kasuwa sun nuna rashin amincewarsu ta hanyar rufe kasuwar da taruwa a masallatai ko kuma shiga cikin masu muzaharar.


Inda ya barke har da kashe mutane a hannun

Jami'an tsaro da aka girke a tsakiyar birnin Qum da Tehran inda sukai yi luguden wuta kan masu zanga-zangar.


An ci gaba da zanga-zangar a wannan rana da kwana biyu, inda aka kashe mutane da dama da jikkata wasu.


Mutane sanye da likkafani wadanda suka je Tehran don nuna goyon baya ga Imam Khumaini, sun fuskanci hafsoshin soji a gadar Bagharabad, an kashe wasu da dama daga cikinsu, da jikkata wasu.


Imam Khumaini:

Ina shelanta ranar sha biyar ga watan Khordad a matsayin ranar zaman makoki na jama'a har abada, don tunawa da shahidanmu a wannan rana mai girma, zan ci gaba da zaman makokin a makarantar Faiziyah da fatan da yardar Allah ta'ala za a tumbuke sauran rubabben tushen mulkin mallaka. Kuma tsarin jamhuriyar Musulunci a bisa tsarin Alkur'ani Mai Tsarki ya tabbata a kasarmu."


Imam Khumaini, Sahifah Noor, juzu'i na 7, shafi na 50

 

Imam Khumaini ya samu fitowa a ranar 15 ga Farvarden, 1343, bayan zagayowar waki'ar Faiziyyah da kuma gabanin Dhu-Hijja da Muharram Imam Khumaini ya karbi sakon 'yancinsa ya bar Qaitariya tare da koma gidansa da ke Qum.


Labarin sakinsa ya haifar da Farinciki tare da tura maziyartan Kum da sauran garuruwa zuwa gidansa. Haka nan kuma gwamnatin ta nun sakin Imam ne sakamakon maslahar addini da kuma girmama mahukuntan gwamnati.