Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

4 Yuni 2023

02:11:08
1371002

Jerin Shirye-shiryen Da Ake Cigaba Da Gabatarwa Don Tunawa Da Shekaru 34 Da Wafatin Imam Khumain Qs

Tarbiyya Da Koyar Da Yara Da Samari A Cikin Maganganun Imam Khumaini (Qs)

Jerin Shirye-shiryen Da Ake Cigaba Da Gabatarwa Don Tunawa Da Shekaru 34 Da Wafatin Imam Khumain Qs

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya kawo maku takaitattun maganganu da Imam Khumain Qs yayi a lokacin rayuwarsa zuwa ga al'umma wanda syka kunshe da darussa da dama na zamantakewa, ilimi, gwagwarmaya tabbatar da adalci acikin al'ummah.

Malaman makaranta su kara kula da wadannan yara a ko da yaushe, domin yara su ne fata da makomar wannan al’umma, kuma daga ’ya’yan yau ne ake yin malamai da mazan gobe, su ne za su tafiyar da kasarmu nan gaba.

02/05/2023


* "Dole ne ku samar da wani sabon yanayi a dukkan sassan kasar Iran ta hanyar tsarkake ilimi daga tushen al'adun mulkin mallaka, don mayar da yaranmu kanana a matsayin wani bangare na goyon bayan da a kodayaushe ke tsayawa a bayan fafutukar adawa da Amurka, yahudawan sahyoniya da dukkan 'yan ta'adda daga cikin 'yan ta'addan gabas da yamma, kuma ku tabbata cewa Khumaini zai ci gaba da kasancewa tare da ku a cikin ganuwar gwagwarmaya har sai an tumbuke tushen mulkin mallaka na gabashi da yamma. (2/19/1979)


* "Idan koyarwa ta kasance ita kadai ba tare da tarbiyya ba, to babu fa'ida a cikinta, sai dai wani lokacin yana cutarwa ma haka kuma tarbiyya ba tare da koyarwa ba, domin basu iya yin 'ya'ya su kadai, to ya zama wajibi ilimi da koyarwa su kasance tare da tarbiyya dole su zama tagwaye suna masu tarayyar juna. Domin da mutanen da ba su da ilimi da tarbiyya da sun kasance cikin naui dabbobi idan mutane suka kasance ba tare da Ilimi da tarbiyya ba to sun fi dukkan dabbobi muni (12/7/1979)


* “Dole ne ku kula da tarbiyyar wadannan yaran da kuke kula da tarbiyyar su dole ne ya zamanto tarbiya ce ta addini da kyawawan halaye, don haka idan kuka samar wa al’umma ’ya’ya masu addini, za ku ga yaron mai addini da jajircewa zai gyara al’umma. kuma akasin haka, idan - Abun Allah Ya kiyaye - ya fita daga hannunku - ku malamai - dalibai batattu zasu lalatar da al'umma ne, kuma za ku kasance kune da alhaki. " (11/6/1979)


* “Malaman makaranta su kara kula da wadannan yara a koda yaushe, domin yara su ne fata da makomar al’ummar nan, kuma daga yaran yau an mayar da su malamai da mazan gobe, domin wadannan su ne za su tafiyar da daularmu a nan gaba, kuma dole ne su kare ’yancinmu da zabinmu a bayanmu, don haka malamai su girmama wadannan yara Matasa (matasa) kada su bari su gurbata da abubuwan da mu manya muka gurbata da su, matukar suna kanana kuma kubutattu.

Ina son su kamar yadda kuke son masoyanku, dukansu masoyana ne kuma hasken idanuwana ababen fatana anan gaba.” (9/23/1979)


* "Idan malamai ba su ilimantu da tarbiyantu ba yadda ya dace to ba za su iya ilmintar da tarbiyyantar da matasan ba, domin duk abin da mutum zai yi yana fitowa ne daga mutum asalin zatinsa, sai ku fara 'yan uwa ku fara gyara kanku." kuma ina fatan za ku yi hakan - kuma dukkanmu muna cikin wannan al'amari - har ku iya gyara al'umma." 

(1/7/1980)


* Tarbiyya da karantarwar mutane dole ne ta zama tagwaye, kuma ya zamo tarbiyar ta yan adamtaka, watau wacce ke dauke da matsalolin dan Adam, haka nan ilimi ya zama tarbiyyar da aka ambaci Allah a cikinsa, mai shiryarwa da ikhlasi saboda Allah Maɗaukakin Sarki, da matsayi a cikin hidimar ɗan Adam, kuma ku kula, ya ku madaukaka, ku da sauran waɗanda za su yi hidima ga wannan babban al'amari da wannan babban aikin ibada, ku nuna wa malamai hidimar makarantun da za'a assasa wanda aka kafa a dukkan sassan jamhuriyar Muslunci, in Allah ya yarda, da cewa su koma ga Allah, kuma koyarwarsu tafarkin Allah ne kawai, don biyayya ga Allah”

 (12/27/1981).


* “Ya kamata iyaye mata da Iyaye maza su lura da cewa shekarun matakin makaranta da na jami’a shekaru ne na samartaka ga ya'yansu, kuma za a iya jan hankalinsu zuwa ga gurbatattu da karkatattun kungiyoyi cikin saukin kai, su bar makarantar sakandare cikin sauki, Dalibai su mai da hankali da kuma ba wa kansu cikakken shiri tsaf don kada wakilan kasashen waje su jefa su a hannun Gabas da Yamma da sunan Musulunci na hakika.” (23/9/1981).


* "yin sakaci wajen koyarwa da tarbiyya ha'inci ne ga Musulunci da Jamhuriyar Musulunci da kuma cin amanar al'adun al'ummar kasa da kasa, don haka wajibi ne a yi taka tsantsan a kan haka." (5/12/1978))